Mukarraban Biden Sun Yi Watsi Da Saka Kungiyar (Alhuthi) Cikin ‘Yan Ta’adda Da Trump Ya Yi

Wasu daga cikin manyan mukarraban
zababben shugaban kasar Amurka mai jiran gado Joe Biden, sun yi kakkausar suka
dangane da saka kungiyar Ansarullah (Alhuthi) cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda da
gwamnatin Trump ta yi.
Tashar RT ta bayar da rahoton cewa,
a cikin wani bayani da ya wallafa a shafinsa na twitter, mutumin da ake sa ran
zai rike matsayin shugaban majalisar tsaron kasa a Amurka a cikin gwamnatin Joe Biden, Jake Sullivan,
ya bayyana cewa saka kungiyar Alhuthi cikin ‘yan ta’adda da Trump ya yi, zai
jefa miliyoyin mutane a kasar Yemen cikin hali mafi muni daga wanda suke ciki.
Ya ce bai san dalilin daukar wannan
matakia cikin kwanakin karshe na gwamnatin
Trump ba, domin hakan ba abu ne da zai taimaka wajen warware matsalar rikicin
da ake fama da shi a kasar Yemen ba, illa kara ruruta wutar rikici, da kuma jefa rayuwar
miliyoyin mutane cikin mawuyacin hali.
Majalisar dinkin duniya da kungiyar
tarayyar turai sun soki gwamnatin Trump dangane da daukar wanann mataki na saka
kungiyar Ansarullah ko (Alhuthi) a cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda, tare da
bayyana hakan da cewa ba daidai ba ne.
Babban jami’in majalisar dinkin duniya
kan harkokin agaji ya ce wannan matakin na gwamnatin Trump, zai kawo cikas ga ayyukan
kai agaji da dauki ga miliyoyin al’ummar Yemen, kasantuwar kungiyar Ansarullah
bangare mai muhimamnci a Yemen da ke kula da bangarori masu yawa da ke cike da
miyoyin al’umma a kasar.
015