Iran Na Kan Bakarta Na Shigar Da Karar Amurka A Kotun Duniya

2021-01-17 09:08:02
Iran Na Kan Bakarta Na Shigar Da Karar Amurka A Kotun Duniya

Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta ce, tana nan kan bakarta na shigar da karar Amurka a gaban kotun duniya ta ICJ.

Da yake amsa tambayar ‘yan jarida a taron mako mako da ‘yan jaridan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, Saeed Khatibzadeh, ya ce tabas wannan batu yana nan kuma tuni Iran ta mika wasika game da wannan anniyar tata ga ofishin jakadancin kasar Swizilland dake nan Tehran wanda ke wakiltar kaddarorin Amurka a Iran.

M. Khatibzadeh, ya ce, idan har Amurka bata daina takurawa jami’an diflomatsiyyar Iran da iyallansu ba to tabbas wannan batu za’a mika shi ga kotun duniya domin ta bi wa Iran kadinta.

Ya ce jama’in diflomatsiyyan Iran, na fuskantar takurawa daga AMurka a kungiyoyin kasa da kasa irinsu MDD da bankin duniya da asusun bayar da lamuni na duniya.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!