Rikicin Cinikayyar China Da Amurka Ya Janwo Asarar Dubban Guraben Ayyuka A Amurka

2021-01-17 09:00:52
Rikicin Cinikayyar China Da Amurka Ya Janwo Asarar Dubban Guraben Ayyuka A Amurka

Wani nazari da cibiyar binciken harkokin tattalin arziki ta Oxford ta gudanar, ya bayyana cewa, rikicin cinikayya tsakanin Sin da Amurka ya jawo asarar guraben ayyukan yi 245,000 a Amurka.

Amma ya kuma bayyana cewa, idan bangarorin biyu suka kawar da manufofinsu na saka wa juna karin haraji da inganta cinikayya a tsakaninsu, za a samu sabbin guraben ayyukan yi 145,000 a Amurka ya zuwa 2025.

Kafar yada labarai ta Reuters ta ruwaito cewa, kwamitin kula da harkokin cinikayya a tsakanin Amurka da Sin ta kasar Amurka (USCBC), ce ta kaddamar da nazarin, wanda cibiyar binciken harkokin tattalin arziki ta Oxford ta gudanar.

USCBC kwamiti ne mai zaman kanta, kuma mambobinsa kamfanonin Amurka ne dake harkokin kasuwanci a Sin, ciki har da Coca Cola da sauran fitattu da kananan kamfanonin Amurka.

An fitar da nazarin ne kwanaki kalilan kafin zababben shugaban Amurka Joe Biden ya kama aiki tare da nazarin manufofin cinikayya na kasar. Duk da Joe Biden ya taba furta cewa, ba shi da shirin sauya manufofin haraji da shugaba Trump ya zartar.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!