Kasar Rasha Ta Yi Watsi Da Zargin Amurka Na Alakanta Iran Da Kungiyar 'Yan Ta'adda Ta Al-Qaeda

2021-01-16 21:59:01
Kasar Rasha Ta Yi Watsi Da Zargin Amurka Na Alakanta Iran Da Kungiyar 'Yan Ta'adda Ta Al-Qaeda

Gwamnatin kasar Rasha ta yi watsi da sabon zargin da gwamnatin Amurka ta yiwa Iran na hadata da kungiyar ‘yan ta’adda ta Al-Qa’eda wacce ta kai harin 11 ga watan Satumban shekara ta 2001 a Amurkan.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta fadawa kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran a safiyar yau Asabar, kan cewa Iran kanta ta sha gamuwa da ayyukan ta’addanci na kungiyoyin ‘yan ta’adda daga cikin har da kungiyar Al-Qaeda, sannan ita ce a kan gaba wajen yakar kungiyoyin ‘yan ta’adda a duniya.

Zakharova ta kara da cewa kasar Iran ta taka rawan a zo a gani wajen yakar kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a kasashen Iraki da Siriya.

A ranar tarlatan da ta gabata ne sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya zargi kasar Iran da zama sabuwar matattaran kungiyar Al-Qaeda, a waton taron ‘yan jarida da ya yayi.

A maida martani ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Javad Zareef ya bayyana cewa, a dai-dai sauran ‘yan kwanaki ikon gwamnatin Trump ta kare, Pompeo yana fushi da gazawar gwamnatinsu wajen durkusar da gwamnatin Iran ta hanyar takunkuman tattalin arziki mafi muni a kan kasar. 19

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!