Uganda:Shugaba Yoweri Museveni Ya Sake Lashe Zaben Shugaban Kasa

2021-01-16 21:38:57
Uganda:Shugaba Yoweri Museveni Ya Sake Lashe Zaben Shugaban Kasa

Hukumar zabe a kasar Uganda ta bada sanarwan cewa shugaban kasa mai ci Yuweri Museveni ya lashe zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a ranar Alhamis da ta gabata.

Tashar talabijin ta Aljazeerah ta nakalto shugaban hukumar zabe na kasar ta Uganda Mai sharia Simon Mugenyi yana fadar haka a yau Asabar.

Mugenyi ya kara da cewa Museveni ya lashe zaben da kuri’u miliyon 5.85 wanda shi ne kashi 58.64 % na yawan kuri’un da aka kada a zaben gaba daya.

Babban abokin hamayyar sa a zaben Bobi Wine ya tashi da kuri’u miliyon 3.48 wanda shi ne kashi 34.83% na yawan kuri’un da aka kada a zaben.

Daga karshe shugaban hukumar zaben ya kammala da cewa kashi 52% na wadanda suka cancanci kada kuri’unsu ne suka kada kuri’unsu a zaben na ranar Alhamis. Sakamakon zaben dai ya kara tsawaita shugabancin Museveni na shekara 35 a kasar Uganda.

Sai dai wani mai magana da yawun Bovi wine, Benjamin Katana ya fadawa Aljazeera jim kadan bayan bada sakamakon zaben kan cewa, zaben na cike da magudi kuma an sace kuri’un masu zabe ne. Don haka jam’iyyarsa zata garzaya zuwa kotu don neman adalci.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!