Najeriya: Yawan Wadanda Suke Kamuwa Da Cutar Korona Yana Dada Karuwa A Kasar

2021-01-16 21:30:41
Najeriya: Yawan Wadanda Suke Kamuwa Da Cutar Korona Yana Dada Karuwa A Kasar

Cibiyar yakar cututtuka ta kasa (NCDC) a tarayyar Najeriya ta bada sanarwan cewa yawan wadanda suke kamuwa da cutar korona a kasar yana karuwa a cikin ‘yan makonnin nan.

A jiya jumma’a dai cibiyar ta bayyana cewa mutane mutane 1,867 ne suka kamu da cutar, wanda shi ne adadi mafi yawa, da aka taba samu a yini guda tun bullar cutar a farkon shekarar da ta gabata.

Jaridar Premim times ta Najeriya ta nakalto bayanan cibiyar NCDC na cewa mutane 23 ne suka rasa rayukansu a jihohi 23 a jiya jumma’a kadai.

Labarin ya kara da cewa a halin yanzu yawan wadanda suka kamu da cutar tun bayan bularta ya kai 107,345 inda 84,535 daga ciki sun warke a yayinda adadin da suka rasa rayukansu ya tashi zuwa mutane 1,413.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!