Iran: Hadin Kai Tsakanin Kasashen Da Amurka Ta Dorawa Takunkumi Zai Taimaka Wajen Faduwar Darajar Dala

2021-01-16 21:22:47
Iran: Hadin Kai Tsakanin Kasashen Da Amurka Ta Dorawa Takunkumi Zai Taimaka Wajen Faduwar Darajar Dala

Kakakin kwamitin tsaro a majalisar dokoki na kasar Iran ya bayyana cewa hadin kai tsakanin kasashen da Amurka ta dorawa takunkuman tattalin arziki zai taimaka wajen faduwar darajar dala a duniya.

Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto Abul-Fadle Amuyi yana fadar haka a lokacin da yake ganawar da shugaban kwamitin kawance na majalisun dokokin Iran da Cuba a yau Asabar.

Amuyi ya kara da cewa gwamnatin kasar Amurka ba zata dai na dorawa kasashen duniya takunkumi a matsayin makami na tursasawa kasashen duniya mika wuya ga bukatunta ba. Don haka kamar yadda kasar Cuba ta tabbata a kan matsayinta shekaru fiye da 60 da suka gabata, sauran kasashen da Amurak ta dorawa takunkumai wadanda suka hada da Iran, Venezuela, Rusha, Belerus, Siriya, Lebanon, Iraki da kuma Yemen zasu bi sawunta.

Amuyi ya ce hada kai tsakanin wadannan kasashe zai zama masomin faduwar karfin dalar Amurka a kasuwannin duniya.

A dai-dai lokacinda sauran kwanaki biyar gwamnatin shugaba Trump ta kawo karshen wa’adinta ta kakabawa ministan harkokin cikin gida na kasar Cuba takunkumin tattalin arziki da sunan take hakkin bil’adama da yake yi a kasarsa. 19

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!