MDD:An samu Raguwar Kwarar ‘Yan Gudun Hijiri A Rabin Karshen Shekara Ta 2020 Saboda Cutar Korona

2021-01-16 21:03:14
MDD:An samu Raguwar Kwarar ‘Yan Gudun Hijiri A Rabin Karshen Shekara Ta 2020 Saboda Cutar Korona

Majalisar dinkin duniya ta bada sanarwan cewa yawan yan gudun hijiran da aka kiyasta zasu kwarara zuwa manya-manyan kasashen duniya tsakanin 2019-zuwa tsakiyar 2020 yana tsakanin miliyon 7-8.

Rahoton ya kara da cewa, hana hana tafiye-tafiye da rufe kan iyakokin kasashen mafi yawan kasashen duniya sanadiyyar cutar Korona, daga cikin watan Maris na shekara ta 2020 ya hana yan gudun hijira fita daga inda suke.

Rahoton ya kara da cewa watanni hudu a jere babu wani dan gudun hijira da ya motsa daga inda yake, saboda rufe kan iyakoki da kuma hana tafiye-tafiye a kasashe fiye da 200 a duniya.

Rahoto ya kammala da cewa a ciki sabon kididdiga da aka gudanar, an gano cewa yawan ‘yan gudun hijira a kasashen duniya ya kai miliyon 281 a shekara ta 2020, wanda kuma shi ne kashi 3.6% na yawan mutanen duniya gaba daya.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!