Yemen: An Yi Zanga Zangar Tir Da Sanya Ansarullah A Jerin ‘Yan Ta’adda

2021-01-16 14:51:06
Yemen: An Yi Zanga Zangar Tir Da Sanya Ansarullah A Jerin ‘Yan Ta’adda

Al’mmumar Yemen, sun gudanar da wata zanga zanga ta yin tir da matakin Amurka na sanya kungiyar Ansarullah a cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda na duniya.

Rahotannin daga kasar sun ce an gudanar da zanga zangar ce jiya bayan sallar Juma’a.

Masu zanga zangar dai na raira taken tir da kawancen Amurka da Saudiyya, akan munanen laifukan da suke aikatawa kan al’ummar kasar ta Yemen.

A ranar Litini, data gabata ce gwamnatin Amurka mai barin gado ta sanar da sanya kungiyar ta Ansarullah ta kasar Yemen a cikin jerin kungiyoyin da take alakantawa dana ‘yan ta’adda a duniya.

Kasashen duniya da dama har ma da MDD, sun nuna damuwa akan wannan matakin na Amurka, wanda suka ce zai iya toshe duk wata hanya ta samar da zaman lafiya a kasar te Yemen da yaki ya daidaita, musamman ta fuskar gudanar da ayyukan jin kai.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!