Uganda : Sojoji Sun Yiwa Gidan Bobi Wine kawanya

2021-01-16 14:45:55
Uganda :  Sojoji Sun Yiwa Gidan Bobi Wine kawanya

Jagoran ‘yan adawa kuma dan takara a zaben shugabancin kasar Uganda Robert Kyagulanyi, wanda akafi sani da Bobi Wine ya ce sojoji sun yiwa gidansa kawanya.

Matakin jami’an tsaron ya zo ne sa’o’i bayan da M. Wine yayi ikirarin lashe zaben da ya gudana a ranar Alhamis, tare da yin watsi da sakamakon kidayar kuri’un da ya nuna shugaba mai ci Yoweri Museveni ne ke kan gaba.

M Bobi Wine, ya kuma koka kan cin zarafin magoya bayansa da jami’an tsaro suka yi, da kuma hana wa magoya bayansa kada kuri’a a zaben shugaban kasar.

A wannan Assabar ce ake sa ran hukumar zaben kasar za ta sanar da sakamakon zaben.

‘Yan takara 11 ne suka fafata a zaben kasar ta Uganda, wanda shugaba Museveni mai shekaru 76 ke neman wa’adi na 6 bayan shafe shekaru 34 yana mulki.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!