Hajizadeh: Iran Ta Gwada Wasu Sabbin Makamai Masu Linzami Da Jiragen Yaki Marasa Matuki

Dakarun kare juyin juya hali na
kasar Iran IRGC sun wasu sabbin makamai masu linzami da kuma jiragen yaki
marasa matuki a karin farko, a wani atisayin gwajin makamai masu linzami da
suka fara a jiya Juma’a.
Babban kwamandan dakarun IRGC a
bangaren tsaron sararin samaniyya Brigadier General Ali Hajizadeh ya bayyana
cewa, a wannan atisayin an gwada sabbin makamai masu linzami wadanda Iran ta
kera, wadanda ake sarrafa su daga tazara mai nisa da na’urori na zamani.
Ya ce babban aiki wadannan makaman
shi ne ragargaza tsarin kariya ta sama na rundunar makiya, ta yadda makaman za
su iya ta tarwatsa makaman kariya na makiya da suke girke a doron kasa, ko kuma
bayan harba su a cikin sararin samaniya.
Baya ga haka kauma ya kara da cewa,
an gwada wasu sabbin jiragen yaki marasa matuki masu tsananin sauri da Iran din
ta kera, wadanda za su iya kai hari daga tazara mai nisa, a lokaci guda kuma
suna kauce wa na’urar radar ta makiya ba za ta iya gane su a cikin sararin
samaniya ba.
Ya ce duk wannan yana zuwa ne domin kara zama cikin shirin ko ta kwana domin fuskantar kowace irin barazana daga makiya, tare da tabbatar wa masu tunanin cewa za su iya taba kasar su kwana lafiya da cewa, hakan ba a bu ne mai sauki ba.
015