​Najeriya: Gwamnati Za Ta Sayar Da Wasu Kaddarorinta Domin Cike Gibin Kasafin Kudin 2021

2021-01-16 10:38:04
​Najeriya: Gwamnati  Za Ta Sayar Da Wasu Kaddarorinta Domin Cike Gibin Kasafin Kudin 2021

Gwamnatin tarayyar Najeriya na shirin sayar da wasu daga cikin kaddarorinta domin samar da kudaden da za a cike gibin kasafin kudin shekara ta 2021 da muke ciki.

Bisa ga bayanai da suke fitowa daga majiyoyin gwamnatin tarayyar Najeriya, baya ga shirin karbar rancen kudade daga kasashen ketare da kuma cikin gida, gwamnatin tana shirin saka wasu kadarorin gwamnati a kasuwa, domin a sayar a samu kudaden zubawa cikin kasafin 2021.

Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed, ta tabbatar da shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ke yi domin fara sayar da wasu kaddarorin gwamnati da niyyar samun kudaden da za a yi ayyukan kasafin 2021 da su.

Batun sayar da kadarorin yana cikin wani kundin daftari da gwamnatin tarayya wanda ta mika wa majalisar dokoki, sannan kuma gwamnatin ta ce za a sayar da wasu kadarorin na daban a bangaren harkokin mai.

Dukkanin wadannan bayanai suna a cikin wani daftarin da Ministar Kudade Zainab Ahmed ta mika wa majalisa a ranar Talata da ta gabata.

Tun a ranar 23 Ga Disamba ne dai aka sa wa kasafin kudin hannu, inda aka amince za a kashe naira tiriliyan 13.58, sai dai kuma daga cikin kudaden, naira tiriliyan 5.02 duk bashi ne za a ciwo, sannan kuma za a kashe naira tiriliyan 3.3 wajen biyan basussukan da ake bin Najeriya daga cikin kasafin, sai kuma naira tiriliyan 5.6 da za a kashe wajen biyan albashin ma’aikata, sannan kuma za a kashe naira tiriliyan 4.1 wajen yin manyan ayyuka a cikin kasa.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!