​Yemen: Ansarullah Ta Kirayi Larabawa Masu Yaki Da Al’ummar Yemen Da Su Dawo Hayyacinsu

2021-01-16 10:34:07
​Yemen: Ansarullah Ta Kirayi Larabawa Masu Yaki Da Al’ummar Yemen Da Su Dawo Hayyacinsu

Kungiyar Ansarullah ta yi nasiha ga kasashen larabawan da suka dogara ga Trump wajen samun kariya da taimako domin kisan al’ummar kasar Yemen.

Kakakin kungiyar Ansarullah Muhammad Abdulsalam, ya kirayi dukkanin kasashen da suka dogara da Trump suka fawwala lamarinsu gare shi, da su dawo cikin taitayinsu, domin kuwa ta Trump ta kare.

Abdulsalam ya ce irin wadannan kasashe da suka mayar da komai nasu ga Amurka, musamman ma shugaban kasar mai barin gado Donald Trump, ya ce lokaci ya yi da za su koma cikin hankalinsu, kuma su kawo karshen kisan kiyashin da suke yi a kan al’ummar musulmi a Yemen.

Haka nan ya yi ishara da cewa, a cikin shekaru 6 da Saudiyya da UAE gami da wasu masu yi musu amshin shata suka kawshe suna kisan mata da kananan yara a Yemen tare da cikakken goyon baya da taimako daga Donald Trump da wasu kasashen turai, babu abin da hakan ya Haifa musu illa zubar mutuncinsu a idon duniya, kuma hisabi na jiransu a gobe kiyama.

Rahotannin da majalisar dinkin duniya gami da kungiyoyin bayar da agaji na kasa da kasa suka bayar kan yakin Yemen, sun tabbatar da cewa daga lokacin da Saudiyya ta fara kaddamar yaki kan kasar Yemen shekaru shida da suka gabata ya zuwa, ta kashe dubban farraen hula, tare da rusa dubban gidaje da makarantu da asibitoci gami da masallatai da cibiyoyin kasuwanci.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!