Isra’ila: Biden Ba Zai Yi Watsi Da Siyasar Trump Wajen Hada Alaka Tsakaninmu Larabawa Ba

Majiyoyin gwamnatin Isra’ila sun ce
zababben shugaban Amurka zai ci gaba da bin salon siyasar sanya larabawa su
kulla alaka da Isra’ila kamar yadda Trump ya yi.
Bisa ga rahotanni da kafofin yada labaran
Isra’ila ke bayarwa, majiyoyin gwamnatin yahudawan Isra’ila sun tabbatar cewa,
zababben shugaban Amurka Joe Biden zai ci gaba da bin salon siyasar sanya
larabawa su kulla alaka da Isra’ila.
Rahoton ya kara da cewa, Ilyaf
Benjamin babban jami’i mai kula da harkokin kasashen yankin gabas ta sakiya a
ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ya bayyana cewa, babu batun komawa baya
dangane da batun kulla alaka tsakanin Isra’ila da gwamnatocin larabawa.
Ya ce gwamnati mai barin gado a
Amurka ta taka gagarumar rawa wajen karkatar da hankulan kasashen larabawa zuwa
ga kulla alaka da gwamnatin Isra’ila, haka nan kuma gwamnatin da za ta karbi
ragamar mulki za ta ci gaba da bin wannan siyasa.
Ya kara da cewa yanzu haka suna
tattaunawa da wasu kasashen arewacin Afirka, da suke shirye su kulla irin
wannan alaka da Israila.
Kasashen hadaddiyar daular larabawa
da Bahrain da kuma Sudan gami da Morocco, su ne a halin yanzu dai suka sanar da
kulla alaka hukumance da gwamnatin
yahudawan Isra’ila bisa matsin lambar gwamnatin Trump mai barin gado.