Iran: Jirgin Yaki Na Karkashin Ruwa Ya Jarraba Makamai Masu Linzami Na Karkashin Ruwa A Atisayen “Iqtidar 99”

2021-01-15 15:29:48
Iran: Jirgin Yaki Na Karkashin Ruwa Ya Jarraba Makamai Masu Linzami Na Karkashin Ruwa A Atisayen “Iqtidar 99”

A karon farko wani jirgin yaki na karkashin ruwa wato ‘ Submarine’ na kasar Iran ya jarraba makamai masu linzami na karkashin ruwa samfurin ‘Torpedo’ tare da samun nasara.

Tashar talabijin ta Al-Manar ta nakalto Admiral Hamzah Ali Kaviyani mai magana da yawon sojojin Iran, a atisayin sojojin ruwa da suke gudanarwa a Tekun Omman da mashigar ruwa ta Hurmuz ya na fadar haka a jiya Alhamis.

Admiral Koviyani ya kara da cewa atisayin wanda aka sanyawa suna “Iqtidar 99” ya jarraba makaman Jumhuriyar Mususlunci ta Iran da dama tare da samun nasara a ko wanne daga cikinsu.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!