Indonesia: Girgizar Kasa Mai Karfi Ta Aukawa Tsibirin Sulawesi Inda Mutane Da Dama Suka Rasa Rayukansu

2021-01-15 15:23:11
Indonesia: Girgizar Kasa Mai Karfi Ta Aukawa Tsibirin Sulawesi Inda Mutane Da Dama Suka Rasa Rayukansu

A safiyar yau jumma’a ce girgizar kasa mai karfin ma’aunin richter 6.2 ta aukawa tsibirin Sulawesi na kasar Indonesia, inda ta rusa gine-ginen a asibitin birnin Mamuju kan marasa lafiya da jami’an jinya da suke cikinsa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa akalla mutane 34 ne aka tabbatar da mutuwarsu ya zuwa lokacin bada wannan labarin.

Jami’an jinya a kasar sun fara bincike don gano wadanda suke da sauran shan ruwa a wurare daban-daban a tsibirin.

Ali Rahaman wani jami’in kungiyar bada agaji a birnin Mamuju ya bayyana cewa yawan wadanda suka mutu zai karu don har yanzun suna neman wasu mutane da dama wadanda ba’a suka bace a cikin burbushin gine-ginen da suka rushe.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!