Arsenal Da Crystal Palace Sun Tashi Ba Wanda Ya Ci Wani A Gasar Premier League
2021-01-15 15:06:39

A gasar Premier League wanda ake gudanarwa a kasashen Turai a halin yanzu, kungiyoyin kwallon kafa na Arsenal da Crystal Palace sun tashi ba wanda ya ci wani, wasan a jiya Alhamis da yamma, a karawar da suka yi a filin wasa na Emirate Stadium.
Dukkanin kungiyoyin biyu sun sami damammaki na saka kwallo a raga, amma ba tare da samun nasarar yin haka ba.
A minti na 20 a cikin wasan, Pierre –Emerick ya kusan saka kwallo a raga, amma mai tsare ragar ya hana hakan faruwa, tare da buge kwallon zuwa waje.
A halin yanzu dai kungiyar Arsenal ta na a matsayi na 11Th tare da maki 2 sama da kungiyar Crystal Palace, wacce take matsayi na 13TH.
Tags:
gasar premier league
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!