Iran : Ayyana Ansarullah A Matsayin ‘Yan Ta’adda, Zai Raunana Shirin Samar Da Zaman Lafiya A Yemen

2021-01-14 21:39:29
Iran : Ayyana Ansarullah A Matsayin ‘Yan Ta’adda, Zai Raunana Shirin Samar Da Zaman Lafiya A Yemen

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta maida martani game da matakin Amurka na ayyana ‘yan kungiyar Ansarullah da aka fi sani da ‘yan houstis a Yemen, a matsayin ‘yan ta’adda, wanda ta ce ba zai haifar da da-mai-ido ba a kasar dake fama da rikici.

Da yake sanar da hakan kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, ya ce matakin na Amurka zai raunata duk wani shiri na samar da zaman lafiya a kasar ta Yemen.

Saïd Khatibzadeh, ya kara da cewa duk wani shirin warware rikicin kasar da ayyukan agaji da kuma shirin MDD, na samar da zaman lafiya zasu gamu da cikas, saboda wannan matakin na Amurka na sanya ‘yan houtsis a cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Dama dai a cewarsa kasar ta Yemen, ta fada cikin bala’I mafi muni a duniya, sannan ga wannan matakin na yauta da Amurka ta dauka wanda zai kara wargaza duk wani fata da ake da shi domin warware rikicin kasar.

Ya kara da cewa wannan matakin da gwamnatin Trump, ta dauka a daidai lokacin da take barin gado, wani yunkuri ne kara dagula al’amura da kuma jefa tattaunawar zaman lafiyar Yemen cikin wani hali na rashin tabbas, inji kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran.

Ita ma dai a wannan Alhamis, MDD, ta bukaci AMurka data soke matakin, domin guje wa jefa kasar ta Yemen cikin matsananciyar yunwa.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!