An Yi Wa Afrika Tanadin Allurar Rigakafin Korona Miliyan 270

2021-01-14 21:37:00
An Yi Wa Afrika Tanadin Allurar Rigakafin Korona Miliyan 270

Kungiyar tarraya Afrika (AU), ta ce an yi ma ta tanadin allurar rigakafin cutar korona miliyan 270 domin amfanin al’ummar nahiyar, kamar yadda wata sanarwa kasar Afrika ta Kudu, mai rike da shugabancin kungiyar a wannan karo ta sanar.

Rigakafin wanda akalla za’a samu miliyan hamsin na allurar a tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni, za’a karbe shi ne daga kamfanonin samar da magunguna na Pfizer-BioNTech, da AstraZeneca da kuma Johnson & Johnson.

Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wanda shi ne shugaban kungiyar ta AU, ya ce wannan babu ne mai kyau, wanda zai bamu damar sayan rigakafin da kudinmu a cikin ‘yanci.

Tuni dai aka riga aka cimma matsaya da wasu bankunan Afrika da kuma bankin duniya domin taimakawa kasashen Afrika yadda zasu sayi maganin.

Kungiyar tarayyar Afrika ta ce rigakafin da za’a ba ta a cikin tsarin nan na Covax, a cikin watan nan Janairu zuwa tsakiyar watan Fabarairu, ba zai isa ko jami’an kiwon lafiya ba, balle jama’ar nahiyar a daidai wannan lokacin da aka fuskantar sake dawowan cutar a karo na biyu a wasu kasashe.

Hukumar hana yaduwar cutuka ta AFrika (Africa CDC), ta ce ana bukatar yi wa jama’ar nahiyar kashi 60 cikin dari rigakafin domin takaita yaduwar cutar.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!