Rasha : Amurka Na Kawo Cikas A Yunkurin Sasanta Iran Da Kasashen Larabawa

2021-01-14 21:30:06
  Rasha : Amurka Na Kawo Cikas A Yunkurin Sasanta Iran Da Kasashen Larabawa

Kasar Rasha, ta ce tana neman hanyoyin sansanta Iran da kasashen larabawa na tekun farisa.

Da yake sanar da hakan a wani taron manema labarai a wannan Alhamis ministan harkokin wajen kasar ta Rasha, Sergio Lavrov, ya ce Amurka na iya duk kokarinta na kawo cikas a yunkuri da kasar ke yi na samar da zaman lafiya tsakanin Iran da kasashen larabawa.

M. Lavrov, ya kara da cewa muna fatan Iran, da kasashen tekun farisa su samu hanyar tattaunawa domin magance sabanin dake tsakaninsu, musaman ta fuskar harkar soji, da kuma kuma samar daci gaba ta dukkan fannoni a tsakaninsu.

Saidai a cewarsa har yanzu gwamnatin Amurka, na ci gaba da kawo cikas a yunkurin cimman wannan buri.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!