An Kashe Dakarun Wanzar Da Zaman Lafiya 3 A Mali

2021-01-14 21:27:50
An Kashe Dakarun Wanzar Da Zaman Lafiya 3 A Mali

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD, a Mali, ta sanar da mutuwar dakarunta guda uku a wani hari da aka kai wa tawagar motocinsu a arewacin kasar Mali.

Wata sanarwa da tawagar ta (Minusma), ta fitar ta ce an kai wa dakarun na ta hari ne a ranar laraba a lokacin da suke sintiri a arewacin yankin Bambara, bayan da motarsu ta taka wani abun fashewa.

Lamarin ya yi sanadin mutuwar dakarun tawagar guda uku ‘yan asalin kasar Ivory Coast, da kuma jikkatar wasu bakwai, a cewar majiyoyi daga tawagar.

Tuni dai MDD ta yi tir da harin.

Tawagar (Minisma), dake aiki tun a cikin shekara 2013, a Mali, ta yi hasarar mambobinta sama da 230, wanda 130 daga cikinsu ta hanyar hare hare ne a cewar MDD.

Ita ce kuma wata tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD, data fi samun hasarar rayuka a duniya, sanadin hare haren da ake kai wa ayarin motoci da kuma sansanoninta.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!