Amurka Ta Sanya Wa Cibiya Mai Samar Da Rigakafin Korona Na Iran Takunkumi

2021-01-14 14:45:22
Amurka Ta Sanya Wa Cibiya Mai Samar Da Rigakafin Korona Na Iran Takunkumi

Gwamnatin Amurka mai barin gado ta sanya wa wasu mutane da kuma wasu cibiyoyi na Iran ciki kuwa har da ɗaya daga cikin cibiyoyin da suke samar da rigakafin cutar Korona ta ƙasar takunkumi.

A jiya Laraba ce dai ma’aikatar baitul malin Amurkan ta sanar da wannan mataki, a daidai lokacin da saura mako guda ya rage wa gwamnatin Amurka ta Trump mai ci ta sauka daga karagar mulkin, inda ta ce ta sanya wa wasu mutane biyu da kuma wasu cibiyoyi guda 16 ba ƙasar Iran ɗin cikin takunkumi.

Daga cikin cibiyoyin da aka sanya musu takunkumin har da Cibiyar Astan Quds Razavi, cibiyar da ke kula da haramin Imam Ridha (a.s), Imamin Shi’a na takwas da kuma Cibiyar Danesh Bunyan Barakat, ɗaya daga cikin cibiyoyin da suke samar da rigakafin cutar nan ta COVID-19 na ƙasar Iran.

Sanya wannan takunkumin dai yana daga cikin matakin da gwamnatin Trump ɗin take ɗauka da sunan siyasar takurawa Iran da nufin dunƙufar da ita. To sai dai kuma hakan bai sanya Amurkan cimma manufar ta ba.

Da dama dai suna ganin wannan matakin da Trump ɗin yake ɗauka cikin ‘yan kwanakin da suka rage masa ya sauka daga karagar mulki cikin wulaƙanci a matsayin wani ihu bayan hari wanda ba za su iya sanya shi cimma manufarsa kan Iran ɗin wanda ya gagara cimmawa tsawon shekaru huɗun da suka gabata na mulkinsa ba.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!