Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Ta Kawo Karshen Raɗe-Raɗin Da Ake Yi Kan Ranar Buɗe Makarantu A Kasar

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta kawo ƙarshen kace-nacen da ya kunno kai dangane da ranar da za a buɗe makarantu a duk faɗin ƙasar inda ta sake tabbatar da ranar 18 ga watan Janairun a matsayin ranar da za a buɗe makarantun kamar yadda ta sanar a baya.
Kace nacen dai ya faru ne biyo bayan wata magana da ministan
ilimi na ƙasar Malam Adamu Adamu ya yi ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata inda
aka ruwaito shi yana cewa akwai yiyuwar a yi dubi cikin batun buɗe makarantun a
ranar 18 ga watan Janairun sakamakon matsalar ƙaruwar yaɗuwar cutar COVID-19 a
ƙasar.
Darakta yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na Ma’aikatar ilimi ta tarayyar, Mr. Ben Bem Goong ne yayi wannan ƙarin haske inda ya bayyana
wa manema labarai cewa an yi mummunar fahimta ne ga maganar da ministan yayi ne
kan batun ɓarkewar cutar ta COVID-19 inda ya ce maganar tasa ba tana nufin a ɗage
ranar komawa ɗin ba ne.
Mr. Goong ya ce: Gwamnatin tarayya dai ba ta soke ranar
18 ga watan Janairu a matsayin ranar da za a buɗe makarantun ba, abin ministan ya
ce shi ne akwai yiyuwar a yi dubi cikin ranar bisa la’akari da rahoton da ake da
shi dangane da ci gaba da yaɗuwar cutar ta COVID-19.
Ya ƙara da cewa idan ga misali gobe sai kwamitin
shugaban ƙasa mai sanya kan cutar ya sanar da cewa adadin waɗanda suka kamu da
cutar sun kai 5000 a rana guda, to ai ba za a buɗe makarantu ba, to wannan shi
ne abin da ake nufi da dubi cikin lamarin da ministan yayi magana kai.
A ɓangare guda kuma babban jami’in tsare-tsare na kwamitin shugaban ƙasar, Dr. Sani Aliyu ya tabbatar da cewa za a buɗe makarantun a ranar 18 ga watan Janairun.