Qalibaf: Dawowa Yarjejeniyar Nukiliya Bai Wadatar Ba, Wajibi Ne Amurka Ta Cire Wa Iran Dukkanin Takunkumi

2021-01-14 09:14:27
Qalibaf: Dawowa Yarjejeniyar Nukiliya Bai Wadatar Ba, Wajibi Ne Amurka Ta Cire Wa Iran Dukkanin Takunkumi

Shugaban majalisar shawarar musulunci ta ƙasar Iran, Muhammad Baqer Qalibaf ya bayyana cewar yiyuwar dawowar Amurka cikin yarjejeniyar nukiliyan bayan ɗarewar karagar mulkin sabuwar gwamnatin ƙasar ba shi da wani muhimman matuƙar dai ba a ɗage wa Iran ɗin dukkanin takunkumin da aka sanya mata ba.

Shugaban majalisar dokokin na Iran ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da shafin watsa labarai na Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei inda ya ce tun asali ma manufar ƙulla yarjejeniyar ita ce ɗage takunkumin da aka sanya wa Iran, don haka matuƙar dai ba a ɗage takunkumin ba, dawowar Amurka cikin yarjejeniyar ba shi da wani amfani.

Mr. Qalibaf ya ci gaba da cewa: Matuƙar Amurka tana son komowa cikin yarjejeniyar nukiliyan, wajibi ne ta fara da soke takunkumin da ta sanya wa Iran bayan ta fice daga yarjejeniyar sannan kuma ta sauke nauyin da ke wuyan karkashin yarjejeniyar.

Sai dai shugaban majalisar shawarar Musuluncin ta Iran ya ja kunnen cewa wajibi ne Iran ta gani a kas cewa lalle an ɗage takunkumi ba kawai maganar fatar baki cewa an ɗage ba amma kuma a aikace babu abin da aka gani a kas.

Waɗannan kalamai na Mr. Qalibaf ɗin suna zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa matsayar Iran dai dangane da batun dawowar Amurka cikin yarjejeniyar nukiliya shi ne wajibi ne Amurkan ta ɗage dukkanin takunkumin da ta sanya wa Iran a aikace ba wai kawai maganar dawowarta ta fatar baki ba wanda Jagoran ya ce Iran ma ba wai tana hanzari wajen ganin Amurkan ta dawo cikin yarjejeniyar ba ne, face dai abin da ke da muhimmanci a wajenta shi ne ɗage takunkumin.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!