Sama Da Mutane 80 Ne Aka Kashe A Hare-Haren Baya-Bayan Nan A Yammacin Kasar Habasha

2021-01-14 09:11:28
Sama Da  Mutane 80 Ne Aka Kashe A Hare-Haren Baya-Bayan Nan A Yammacin Kasar Habasha

Hukumar kare haƙƙoƙin bil’adama ta ƙasar Habasha (Ethiopia) ta bayyana cewar sama da fararen hula 80 ne, ciki kuwa har da ƙananan yara, aka kashe a harin baya-bayan nan da aka kai yammacin ƙasar da ke fama da rikici.

Kakakin hukumar ta Ethiopian Human Rights Commission (EHRC), Aaron Maasho ne ya bayyana hakan inda ya ce kisan gillan ya faru ne a yankin Benishangul-Gumul da ke kan iyaka da ƙasashen Sudan da kuma Sudan ta Kudu.

Kakakin hukumar ta EHRC ya ci gaba da cewa: Mun sami labarin cewa an kashe sama da mutane 80 waɗanda shekarun suka kama daga shekaru 2 zuwa 45 biyo bayan hare-haren da aka kai yankin.

Har ya zuwa yanzu dai babu wata ƙungiya ko jama’a da suka ɗauki alhakin kai wannan harin, sai dai mahukuta suna ci gaba da bin diddigin lamarin inji shi.

Yankin da aka kai harin dai yana fuskantar hare-hare da kuma tashin hankulan cikin ‘yan watannin da suka gabata din nan wanda ake fassara hakan a matsayin wani rikici na kabilanci da ke gudana tsakanin kabilun da suke wajen.

Gwamnatin Habashan dai t ace tana iyakacin ƙoƙarinta wajen tabbatar da doka da oda a wajen amma har ya zuwa yanzu lamurra ba su daidaita ba duk kuwa da ziyarar da firayi ministan ƙasar Abey Ahmad ya kai wajen har sau biyu.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!