Mo Salah Ya Ba Da Taimakon Motar Daukar Marasa Lafiya Don Taimakon Masu Cutar COVID-19

2021-01-14 09:04:58
Mo Salah Ya Ba Da Taimakon Motar  Daukar  Marasa Lafiya Don Taimakon  Masu Cutar  COVID-19

Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ɗan ƙasar Masar kuma mai buga wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta Ingila, Mohammad Salah ya ba da taimakon motar ɗaukar marasa lafiya da kuma kututun iskar oxygen ga mahukuntan ƙauyansu don taimakawa mutanen da suka kamu da cutar nan ta COVID-19 a ƙauyen a daidai lokacin da ƙasar Masar ɗin take fuskantar sake dawowar cutar a ƙasar.

Shugaban ƙungiyar ba da agaji ta Mohamed Salah Charity Foundation Hasan Bakr ne ya sanar da hakan inda ya ce duk da cewa dan wasa yayi nisa da gida amma yana da alaƙa da mutanen ƙauyen musamman marasa abin hannu inda a kowace shekara ya kan ware kudaden da suka kai dala 64,000 don taimakawa mutanen ƙauyen.

Jami’in ya ƙara da cewa a halin yanzu suna da kututun oxygen guda 14 a cibiyar agajin waɗanda ake amfani da su wajen taimakon mutanen ƙauyen Nagrig (wato ƙauyen da aka haifi Mo Salah ɗin) da ma mutanen ƙauyukan da suke makwabtaka da wajen, bugu da ƙari kan motar ɗaukar marasa lafiyan da ya bayar, wanda hakan ya taimaka nesa ba kusa ba wajen kula da waɗanda suka kamu da cutar ta Coronavirus.

A watan Nuwamban bara ne dai aka samu Muhammad Salah, ɗan shekaru 28 a duniya, da cutar ta COVID-19 bayan gwajin da aka yi masa. Sai dai tuni ya samu sauƙi daga cutar.

Kasar Masar dai tana daga cikin ƙasashen Afirka da cutar ta Coronavirus ta fara ɓulla a can kuma ya zuwa yanzu akwai mutane 150,753 da suka kamu da cutar sannan wasu 8,249 kuma sun mutu tun bayan ɓullar cutar sama da watanni goman da suka gabata.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!