Amurka: ​Majalisar Wakilai Ta Fara Zama Domin Tattauna Batun Tsige Donald Trump

2021-01-13 19:55:57
Amurka: ​Majalisar Wakilai Ta Fara Zama Domin Tattauna Batun Tsige Donald Trump

Majalisar wakilan kasar Amurka ta fara gudanar da zama domin tattauna batun tsige Donald Trump daga kan karagar shugabancin kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, yanzu haka majalisar wakilan kasar Amurka ta fara gudanar da zamanta, domin tattauna batun tsige Donald Trump daga kan karagar shugabancin kasar Amurka, inda za a kada kuri’a kan wannan batu.

‘Yan majalisar jam’iyyar Democrat da ke da babban rinjaye a majalisar wakilan suka gabatar da wannan daftarin kudirin, bisa zargin Trump da tafka manyan laifuka da suka sabawa kundin tsarin mulkin kasar, da ma kokarin rusa tsarin demukradiyyar kasar Amurka, ta hanyar tunzura magoya bayansa wajen kaddamar da hari kan majalisar dokokin kasar a lokacin da majlisar ke gudanar da zama, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5 da suka hada har da jami’in ‘yan sanda.

Shugabar majalisar wakilan kasar ta Amurka Nancy Pelosi ta bukaci mataimakin shugaban kasar ta Amurka Mike Pence da ya yi amfani da doka ta 25 a cikin kundin tsarin mulki, wadda ta bayar da damar tsige shugaban kasa idan ya tafka wani laifi, inda mataimakinsa zai rike mukamin na rikon kwarya, amma Pence yaki amincewa da hakan.

Bisa laifukan da Trump ya aikata da suka hada da ingiza magoya bayansa domin kaddamar da farmaki kan ginin Capitol inda majalisar dokoki take, majalisar wakilan na son yin amfani da wanna damar domin gurfanar da Trump, ta yadda ba zai kara rike wani mukamin gwamnati a kasar Amurka ba har karshen rayuwarsa.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!