​EU Ba Ta Amince Da Saka Ansarullah Ta Yemen Cikin ‘Yan Ta’adda Ba

2021-01-13 19:53:04
​EU Ba Ta Amince Da Saka Ansarullah Ta Yemen Cikin ‘Yan Ta’adda Ba

Kungiyar tarayyar turai ta yi watsi da matakin da Amurka ta dauka na saka kungiyar Ansarullah ko kuma Alhuthi a cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Shafin yada labarai na kungiyar tarayyar turai ya bayar da bayanin cewa, kakakin babban jami’i mai kula da siyasar wajen kungiyar Peter Stano ya bayyana cewa, daukar wannan mataki na saka kungiyar Ansarullah cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda ba abu ne da kungiyar tarayyar turai za ta amince da shi ba.

Ya ce Amurka ta sani sarai kan cewa, daukar wannan mataki babu abin da zai kara haifarwa a kasar Yemen sai kara dagula lamurra, maimakon daukar matakin da zai taimaka wajen warware matsalolin siyasar kasar ta hanyar sulhu da fahimtar juna tsakanin dukkanin al’ummomin kasar.

Daga karshe ya ce kungiyar tarayyar turai tana maraba da duk wani mataki da zai kara kusanto da al’ummomin Yemen wuri guda, maimakon tarwatsa su da kara rarraba kawunansu a cikin wannan mawuyacin hali da kasar take ciki.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!