​Masu Kare Hakkin Dan Adam Sun Zargi Faransa Da Kirkiro Dokokin Gallaza Wa Musulmi

2021-01-13 19:32:52
​Masu Kare Hakkin Dan Adam Sun Zargi Faransa Da Kirkiro Dokokin Gallaza Wa Musulmi

Masu kare hakkin bil adama suna zargin gwamnatin Faransa da kirkiro sabbin dokoki da nufin gallaza wa musulmin kasar.

A wata zantawa da ya yi da kamfanin dillancin labaran AFP babban daraktan gudanarwa na kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch Kenneth Roth ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Faransa tana kirkiro sabbin dokoki wadanda suka yi hannun riga da kare hakkokin dan adam.

Ya ce sabbin dokokin da gwamnatin Faransa ta gabatar da daftarin kudirinsu a halin yanzu, da sunan sabbin dokokin tsaron kasa, suna dauke da wasu bangarori wadanda a zahiri ana nufin take hakkokin musulmi ne a kasar.

Babban daraktan gudanarwa na kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ya ce; gwamnatin Faransa ba ta yi adalci ba, idan ta yi wa aikin shadanci da kuma imani na akida kudin goro, domin kuwa bisa dokar kundin tsarin mulkin kasar, dukkanin ‘yan kasa suna hakkin yin aiki da fahimtarsu ta addini.

Tun bayan zanen batunci kan ma’aiki da jaridar kasar Faransa ta sake bugawa a watannin baya, wanda ya fuskanci fushin musulmi a duniya baki daya, gwamnatin Faransa ta gabatar da daftarin kudirin wasu sabbin dokoki da za su takura wa musulmi, da sunan aikin tabbatar da tsaron kasa.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!