Israel Ta Kai Sabbin Hare-Hare Kan Yankin Kudu Maso Gabacin Kasar Siriya

2021-01-13 08:45:57
Israel Ta Kai Sabbin Hare-Hare Kan Yankin Kudu Maso Gabacin Kasar Siriya

Gwamnatin kasar Siriya ta bada sanarwan cewa, sojojin yahudawan Isra’ila sun kai hare-hare ta sama a kan yankin kudu masu gabacin kasar a safiyar yau Laraba.

Kamfanin dillancin labaran SANA na gwamnatin kasar Siriya ga kada had cewa, hare-haren saun auku ne a kan garuruwan Dyar-Zawr da kuma Bukamal wadanda suke kan iyakar kasar Siriya da Iraqi.

Labarai ya kara da cewa har yanzun ba’a san idan akwai wadanda suka jikata ko suka yi shahada ba.

SANA ta kara da cewa makaman sun fada kan wadannan garurtuwa ne da misalign karfe 01.01 na daren yau.

Kafin haka dai garkuwan makamai masu linzami na kasar ta Siriya suna kakkabo makaman da Isra’ila take kai hare-haren da su.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!