Zarif, Ya Yi Watsi Da Zargin Pompeo Kan Cewa Iran Ce Sabon Sansanin Al’Qaida

2021-01-12 21:40:03
Zarif, Ya Yi Watsi Da Zargin Pompeo Kan Cewa Iran Ce Sabon Sansanin Al’Qaida

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar musulinci ta Iran, Muhammad Jawwad Zarif, ya yi watsi da zargin sakataren harkokin wajen Amurka na baya bayan nan kan cewa, Iran ta zama sabon sansanin kungiyar Al’Qaida.


Mike Pompeo, ya bayanna a wannan Talata cikin wani jawabi cewa’’ sabon sansanin kungiyar al’qaida a yanzu shi ne Iran, fiye da Afganistan bayan harin 11 ga watan Satumban 2001. batun da ministan harkokin wajen kasar ta Iran, ya bayyana da cewa bai da tushe balle makama, hasali ma rashin ta fada ne.


Kalaman na Pompeo, na zuwa yayin da ya rage wa wa’adin gwamnatin Trump, kwana takwas, wanda masu sharhi da dama ke ganin tamakar nade tabarbar kunya ne.


024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!