Uganda Ta Bada Umarnin Dakatar Da Shafukan Sada Zumunta
2021-01-12 21:30:30

Hukumomi a Uganda sun bukaci kamfanonin dilancin intanet a kasar dasu
toshe shafukan sada zumunta da kuma na sakwanni.
Wata wasika da hukumar kula da kamfanonin sadarwa na kasar ta fitar ta bukaci da a toshe shafukan ba tare da wata wata ba.
Matakin ya shafi shafukan sada zumunta da suka hada da Facebook,Twitter, WhatsApp, Signal da kuma Viber.Wannan matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage kwana biyu a je zaben shugabancin kasar, inda za’a fafata tsakanin shugaban kasar, Yoweri
Museveni, da kuma babban abokin hammayarsa, Robert Kyagulanyi, wanda aka fi sani da Bobi Wine.
024
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!