Iran : Babu Zancen Sake Tattaunawa Kan Yarjejeniyar Nukiliya

2021-01-12 21:26:50
Iran : Babu Zancen Sake Tattaunawa Kan Yarjejeniyar Nukiliya

Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta sake nanata cewa babu zancen sake tattaunawa akan yarjejeniyar nukiliyar data cimma da manyan kasashen duniya a shekarar 2015.

Da yake bayyana hakan a taron mako mako ga ‘yan jarida, kakakin gwamnatin kasar ta Iran, Ali Rabiei, ya ce kawai bangarorin da suke cikin yarjejeniyar su mutunta alkawuran da suka dauka.

Mista Rabiei, ya ba bukatar sake yin wata tattaunawa game da yarjejeniyar.

Dama dai a cewarsa tun tuni kasashen Iran, da Rasha da kuma China, sun riga sun nuna adawarsu a game da shirin yin wata sake tattaunawa.

Saboda haka kasashen Faransa, Jamus da kuma Biritaniya, su cika alkawuran da suka dauka baya bukatar sai an sake wata tattaunawa.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!