Zarif: Dole Ne Korea Ta Kudu Ta Gaggauta Sakin Kudaden Kasar Iran Da Ta Tsare

2021-01-12 13:54:35
Zarif: Dole Ne Korea Ta Kudu Ta Gaggauta Sakin Kudaden Kasar Iran Da Ta Tsare

Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya bukaci gwamnatin Korea ta Kudu ta gaggauta sakin kudaden kasar Iran wadanda ta tsare a cikin bankunan kasar don biyayya ga takunkuman kasar amurka a kan kasar.

Ministan ya bayyana haka ne a ganawarsa da Choi Jong Kun mataimakin ministan harkokin wajen kasar Korea ta Kudu wanda yake ziyarar aiki birnin Tehran, dangane da jirgin ruwan kasar da kasar Iran ta kama.

Dangane da jirgin ruwan kasar Korea ta Kudu wanda sojojin ruwa na kasar Iran suka kama saboda sabawa dokokin tsabtar muhalli a tekun farisa kuma, zarif ya ce matsala ce ta kutu, don an rika an shigar da kara a gaban wata kuliya a nan kasar Iran don duba batun.

Jirgin ruwan kasar Korea ta Kudu mai suna HANKUK CHEMI ya fito ne daga kasar Saudia dauke da sinadaran man fetur wadanda yawansu ya kai ton 7,200 a lokacin sojojin ruwa na kasar Iran suka kama shi saboda gurbata ruwan tekun farisa.


19

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!