Libya: An Bada Shawara Kan Yadda Za’a Gudanar Da Zabubbuka A Karshen Shekara Ta 2021

2021-01-12 13:50:46
Libya: An Bada Shawara Kan Yadda Za’a Gudanar Da Zabubbuka A Karshen Shekara Ta 2021

Kwamitin rubuta kundin tsarin mulki na kasar Libya ya gabatar da shawarar yadda za’a gudanar da zabubbuka a cikin watan disamba na wannan shekarar.

Kamfanin dillancin labaran Al-Wasad na kasar ta Libya ne, ya bada wannan labarin. Ya kuma kara da cewa kwamitin rubuta kundin tsarin mulkin ya bayyana haka ne a taron da ya gudanar ta kafar yanar gizo karkashin kula na ofishin jakadancin MDD da ke kasar.

Majiyar MDD a birnin Tripoli ta kara da cewa wannan kwamitin mai mambobi 18 zai sake gudanar da wani taro a cikin mako mai zuwa don tattaunawa kan shawarorin da ya bayar kan yadda za’a gudanar da zabubbukan majalisar dokoki da kuma na shugaban kasa a cikin watan Desamba na wannan shekarar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!