Iran: An Sami Nasara A Mataki Na Farko Na Gwajin Alluran Rigakafin Cutar Korona Kan Mutane
2021-01-12 13:46:50

Mai bawa ministan kiwon lafiya na kasar Iran shawara kan harkokin kiwon lafiya ya bada sanarwan cewa kasashen Iran da Cuba sun sami nasara a gwajin alluran riga kafin cutar korona kan mutanen a mataki na farko da suka yi a nan Iran.
Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto Ali-Reza wahhab-zade yana fadar haka a ranar Lahadi, ya kuma kara da cewa za’a gudanar da mataki na biyu na gwajin ne a kan mutane a kasar ta Cuba.
Wahhab Zade ya kara da cewa idan an kammala ayyukan gwaje –gwajen cikin nasara za’a fara samar da alluran riga kafin ne a cikin kasar Iran.
Cutar Covid 19 dai ta bulla ne a birnin Wuhan na kasar Sin a karshen shekara ta 2019, sannan ya zuwa yanzu ta kama mutane fiye da miliyon 90, a yayinda mutane fiye da miliyon daya da dubu 900 suka rasa rayukansu sanadiyyar kamuwa da cutar a duniya.
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!