Falasdinu: Yawan Falasdinawa Wadanda Suke Kamuwa Da Cutar Korona A Gidajen Yarin Isara’ila Na Kara Yawa

2021-01-12 13:40:49
Falasdinu: Yawan Falasdinawa Wadanda Suke Kamuwa Da Cutar Korona A Gidajen Yarin Isara’ila Na Kara Yawa

Kwamiti mai kula da fursinonin Falasdinawa wadanda suke tsare a gidajen yarin haramtacciyar kasar Isra’ila ya bayyana cewa yawan falasdinawa da suka kama da cutar korona a gidajen yarin yahudawan suna kara yawa.

Tashar talabijin ta “Falastinul-Yaum” ta nakalto kwamitin yana bayyana haka a yau Talata, ya kuma kara da cewa ya zuwa yanzu falasdinawa 191 ne suka kamu da cutar a gidajen yarin yahudawan ya zuwa yanzu.

Labarin ya kara da cewa, nuna halin ko in kula wanda hukumomin haramtacciyar Isra’ila suke yi ne, ya sa yawan Falasdinawan da suke kamuwa da cutar suke kara yawa.

Banda haka kwamitin ya kara da cewa wani fursina bafalasdine mai suna Muhammad Salahuddeen dan shekara 29 a duniya ya yi shahada saboda cutar kansa ko dajin da yake fama da ita a wani gidan yarin yahudawan a cikin yan kwanakin da suka gabataga, saboda rashin kula.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!