Iran: Kungiyoyin Kwallon Kafa Na Esteghlal Da Persepolis Sun Tashi Kunnen Doki A wasan Jiya Litinin

2021-01-12 13:36:11
Iran: Kungiyoyin Kwallon Kafa Na Esteghlal Da Persepolis Sun Tashi Kunnen Doki A wasan Jiya Litinin

A wasanda aka gudanar a jiya Litinin tsakanin manya-manyan kungiyoyin kwallon kafa na kasar Iran wato Esteghlal da kuma Persepolis, wanda kuma aka gudanar a babban filin wasanni na Ozodi da ke nan Tehran, sun tashi kunnen doki 2-2 a wasannin kwallon kafa na cikin gida wanda ake kira “Iran Professional League” ko (IPL).

Wannan shi ne karo na 4 kenan wanda kungiyar Persepolis take yin kunnen doki a wasanninta na wannan kakar.

Esteghlal dai tana matsayin na biyu a jadawalin matsayin kungiyoyin kwallon kafa da suka shiga wasannin tare da maki 19, a yayinda Persepolis take matsayi na 12 tare da maki 12.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!