Gwamnatin Nijeriya Ta Yi Karin Bayani Kan Dalilan Karuwar Cutar COVID-19 Da Ake Samu A Kasar

2021-01-12 09:10:58
Gwamnatin Nijeriya Ta Yi Karin Bayani Kan Dalilan Karuwar Cutar COVID-19 Da Ake Samu A Kasar

Gwamnatin ta bayyana cewar sake buɗe makarantu da wajajen ibadu da ayyuka na addini ba tare da kiyaye dokokin kiwon lafiya sun taimaka wajen yaɗuwar cutar nan ta COVID-19 da ake fuskanta a ƙasar a halin yanzu.

Shugaban kwamitin shugaban ƙasa mai kula da yaɗuwar cutar ta COVID-19, kuma sakataren gwamnatin tarayya ta ƙasar Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a ganawa da manema labarai da suke yi a kai a kai inda ya kara da cewa: sake buɗe filayen jiragen sama da kuma ƙarin tafiye-tafiye na ciki da wajen ƙasar da ake yi a filayen jiragen saman su ma sun taimaka wajen ƙaruwar cutar ta coronavirus tun daga ƙarshe-ƙarshen watan Nuwamban bara ya zuwa yanzu.

Tun dai daga farko-farkon watan Disambar da ta gabata aka fara samun ƙaruwar waɗanda suke kamuwa da cutar ta Corona a Nijeriyan lamarin da ke nuni da cewa ƙasar ta shiga zango na biyu na cutar.

Irin wannan hauhawar ƙaruwar masu kamuwa da cutar ne ya sanya a jiya Litinin Ma’aikatar ilimi ta ƙasar ta sanar da cewa akwai yiyuwar ba za a buɗe jami’oin ƙasar a ranar 18 ga watan Janairun nan kamar yadda aka shirya a baya ba.


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!