‘Yan Majalisar Amurka Sun Buƙaci Biden Da Yayi Watsi Da Sanya Ansarullah Cikin Kungiyoyin Ta’addanci

2021-01-12 08:49:52
‘Yan Majalisar Amurka Sun Buƙaci Biden Da Yayi Watsi Da Sanya Ansarullah Cikin Kungiyoyin Ta’addanci

Wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka sun buƙaci zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka Joe Biden da yayi watsi da matakin da gwamnatin Trump ta ɗauka na sanya ƙungiyar Ansarullah na ƙasar Yemen cikin ƙungiyoyin ta’addanci, suna masu bayyana hakan a matsayin ‘wani yanke hukuncin kisa’ a kan al’ummar Yemen waɗanda suke cikin tsaka mai wuya na yaƙi.

Daga cikin ‘yan majalisar da suka yi wannan kiran har da shugaban kwamitin harkokin wajen na majalisar dokokin Amurka Gregory Meeks wanda ya ce sanya ƙungiyar Ansarullah ɗin a cikin ƙungiyoyin ta’addanci da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yayi a jiya Litinin lamari ne da zai sanya rayuwar al’ummar Yemen cikin tsaka mai wuya da kuma hatsarin gaske.

Don haka ya buƙaci gwamnatin Amurka mai kamawa ta Joe Biden da ta sake dubi cikin wannan lamarin da kuma yin watsi da shi.

A jiya ne dai gwamnatin Amurkan ta sanya kungiyar ta Ansarullah wacce aka fi sani da ‘yan Houthi cikin ƙungiyoyin ta’addanci lamarin da ƙungiyar da ma wasu ƙungiyoyin gwagarmaya na yankin suka yi Allah wadai da shi da bayyana hakan a matsayin ci gaba da zaluntar al’ummar Yemen ɗin da gwamnatin Amurkan take yi ta hanyar nuna goyon baya ga irin ci gaba da zubar da jinin al’ummar da kuma zaluntar su da kasar Saudiyya take jagoranta cikin yakin da ta ƙaddamar kansu.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!