​Iran Ta Bukaci INTERPOL Da Ta Kame Mata Wasu Mutane 4 Masu Hannu A Kisan Sulaimani Da Fakhrizadeh

2021-01-11 19:25:02
​Iran Ta Bukaci INTERPOL Da Ta Kame Mata Wasu Mutane 4 Masu Hannu A Kisan Sulaimani Da Fakhrizadeh

Gwamnatin Iran ta bukaci hukumar ‘yan sanda ta kasa da kasa Interpol, da ta kame mata wasu mutane hudu, wadanda suke da hannu kai tsaye a kisan Kasim Sulaimani da Fakhrizadeh.

Rundunar ‘yan sanda ta kasar Iran ta sanar da cewa, an mika sunayen mutanen hudu wadanda aka tabbatar da cewa suna da hannu kai tsaye wajen shirya kisan da aka yi wa Kasim Sulamani, da kuma Muhsen Fakhrizadeh.

Bayanin ya ce bisa ga doka ta kasa da kasa, akwai matakai na kame masu laifi da hukumar Interpol take yin amfani da su, akwai matakin da bai zama wajibi ta yi aiki da bukatar kame wani ba, akwai matakin da kuma dole ne ta yi aiki da shi, wanda kuma a bisa wannan matakin na karshe ne aka mika wannan bukata.

Gwamnatin kasar Iran dai ta sha alwashin cewa sai ta bi kadun kisan da aka yi wa manyan jami’an nata guda guda biyu, wato Janar Kasim Sulaimani, wanda gwamnatin Amurka da umarnin Donald Trump ta kashe a farkon shekarar da ta gabata a cikin kasar Iraki.

Sai kuma masanin nukiliya Muhsen Fakhrizadeh, wanda shi ma aka kashe ranar 27 ga watan Nuwamban da ya gabata a cikin birnin Tehran, wanda kuma tuni Iran din ta dora alhakin hakan a kan gwamnatin yahudawan Isra’ila, kuma har yanzu Isra’ila ba ta musunta hakan ba.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!