​Pelosi Ta Ce Babu Gudu Babu Ja Da Baya Dangane Da Batun Yunkurin Tsige Trump

2021-01-11 19:21:26
​Pelosi Ta Ce Babu Gudu Babu Ja Da Baya Dangane Da Batun Yunkurin Tsige Trump

Rahotanni daga Amurka na cewa, shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi tana ci gaba da kara matsa lamba domin ganin an tsige Trump daga kan mukamin shugaban Amurka.

Nancy Pelosi ta rubuta wa 'yan majalisar dokoki cewa, majalaisar wakilai za ta gabatar da bukatar neman Mista Pence ya yi amfani da sashen doka na 25 a kundin tsarin mulki domin neman a tsige Trump daga mukaminsa, yayin da shi kuma Pence zai zama shugaban rikon kwarya.

Majalisar wakilan na da damar kaɗa kuri'a a ranar Talata. Daga nan kuma sai a bai wa Mista Pence da sauran muƙarrabai kwana guda su yi wani abu kan buƙatar, duk kuwa da cewa har yanzu Mike Pence bai yi wani furuci ko nuna alamar amincewa da hakan ba.

Mike Pence mataimakin shugaban kasar Amurka, ya yi tir da Allawadai da abin da Donald Trump ya yin a ingiza magoya bayansa har suka kaddamar da farmaki kan majalisar dokokin kasar, wanda hakan ya jawo asarar rayuka da kuma keta hurumin majalisar dokokin kasar.

Idan har Mike Pence ya ki amincewa da tsige Trump, majalisar wakilai za ta kada kuri’ar tsige shi, bayan amincewa da hakan, za a mika batun ga majalisar dattijai, idan kashi biyu bisa uku na ‘yan majalisar dattijan suka amince da haka, to za su kira Trump domin ya gurfana a gabansu, bayann nan kuma za a tabbatar da mataimakinsa a matsayin shugaban rikon kwarya.

Wasu rahotanni daga kasar ta Amurka na cewa a ranar Laraba mai zuwa majalisar wakilan Amurka za ta gudanar da zama kan wannan batu.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!