An Fara Shari’a Wa Wani Hamshaƙin Mai Kuɗin ‘Isra’ila’ Bisa Zargin Rashawa Kan Lu’u-Lu’un Kasar Guinea

2021-01-11 14:41:24
An Fara Shari’a Wa Wani Hamshaƙin Mai Kuɗin ‘Isra’ila’ Bisa Zargin Rashawa Kan Lu’u-Lu’un Kasar Guinea

An fara shari’ar da ake yi wa hamshaƙin mai kuɗin nan Ba’Isra’ile, Beny Steinmetz, da ake zargi da aikata ba daidai da kuma ba da rashawa da cin hanci don ya samu haƙƙin tonon albarkatun ƙasa da suka da lu’u-lu’u a ƙasar Guinea a wata kotu a birnin Geneva a yau ɗin Litinin.

Shari’ar dai wacce aka buɗe ta da safiyar yau Litinin a wata kotun shari’ar laifuffuka ta birnin Geneva na ƙasar Switzerland ana zargin Mr. Steinmetz ne da ba da rashawa ta miliyoyin daloli ga wasu manyan jami’an ƙasar Guinea don ya samu haƙƙin tono ma’adinai da albarkatun ƙasa a ƙasar.

Bayan gudanar da bincike na tsawon shekaru shida, a watan Augustan 2019 ne dai masu shigar da ƙara a birnin Genevan suka zargi hamshaƙin Ba’israilen da laifin ba da rashawa ga wasu manyan jami’an ƙasar Guinea da kuma ƙirƙiro takardu na bogi.

Masu shigar da karar dai suna zargin Mr. Steinmetz da wasu abokan kasuwancinsa su biyu da ba da cin hanci mai tsokar gaske ga matar tsohon shugaban ƙasar Guinea Lansana Conte da wasu jami’ai na daban don su sami damar ikon haƙo ma’adinai a yankin Simandou da ke kudu masu gabashin ƙasar.

Masu shigar da ƙarar sun ce an ba da kimanin dalar Amurka miliyan 10 a matsayin cin hanci ta hanyar amfani da wasu asusun ajiyar banki na ƙasar Swiss, sannan kuma daga baya an ba wa Mr. Steinnmetz wannan haƙƙi na haƙo ma’adinai jim kaɗan kafin Mr. Conte ya mutu a shekara ta 2008.

A baya dai a shekara ta 2019, Mr. Steinmetz ya cimma wata yarjejeniya da gwamnatin Guinea na ta ɗauke masa zargin rashawar da ake masa, shi kuma a nasa ɓangaren zai janye haƙƙin tonon ma’adinan da yake da shi a wannan yankin. To sai dai duk da hakan mahukuta a kasar Swiss suna ci gaba da ƙoƙarinsu na ganin an ci gaba da shari’ar wanda zai iya kai Mr. Steinmetz ga gidan yari na tsawon shekaru 10.

An jima dai ana zargin hamshaƙan masu kuɗin ‘Isra’ila’ da rashawa da cin hanci da nufin mamaye albarkatun ƙasar da ake da su a ƙasashen Afirka.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!