NCDC: Waɗanda Suka Kamu Da Cutar COVID-19 A Nijeriya Sun Dara Mutane 100,000

Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Nijeriya (NCDC)
ta sanar da cewa wasu mutane 1,024 sun kamu da cutar COVID-19 a jiya Lahadi a
ƙasar lamarin da ya sanya adadin waɗanda suka kamu da cutar a ƙasar ya ɗara
mutane 100,000.
Rahotanni daga Nijeriyan sun ce a sanarwar da
hukumar ta NCDC ta fitar a daren jiya Lahadi ta ce cikin sa’oi 24 da suka
gabata kimanin mutane 1,024 ne aka tabbatar da sun kamu da cutar bayan gwajin
da aka musu lamarin da ya sanya adadin waɗanda suka kamu cutar tun bayan farkon
ɗullarta a watan Fabrairun bara ya kai
mutane 100,087.
Har ila yau kuma sanarwa ta ƙara da cewa mutane
8 sun mutu a jiya Lahadin sakamakon kamuwa da cutar lamarin da ya sanya adadin
waɗanda suka mutu sakamakon cutar ya kai mutane 1,358 a duk faɗin faɗin ƙasar.
A ranar Juma’ar da ta gabata ce dai ta zamanto
ranar da aka fi mutuwa a Nijeriya sakamakon cutar Koronan inda mutane 12 suka
mutu.
Mahukuta a Nijeriya ɗin suna ɗora alhalin yawan mace-mace da ake yi a ƙasar sakamakon cutar da gangancin mutane da kuma jinkiri wajen tafiya asibiti yayin da mutum ya ji alamomin cutar a tattare da shi.