Habasha Ta Ce Ta Kashe Da Kuma Kama Wasu Jami’an TPLF ‘Yan Aware Na Yankin Tigray

2021-01-11 14:14:47
 Habasha Ta Ce Ta Kashe Da Kuma Kama Wasu Jami’an TPLF ‘Yan Aware Na Yankin Tigray

Dakarun gwamnatin Habasha sun ce sun kashe da kuma kama wasu membobin jam’iyyar Tigray People’s Liberation Front (TPLF) ta ‘yan tawayen yankin Tigray na ƙasar a wasu sabbin hare-hare da suka ƙaddamar lamarin da ke nuni da cewa har ya zuwa yanzu dai tsugune ba ta ƙare ba a yankin watanni biyu bayan ɓarkewar asalin rikici a yankin.

Gidan talabijin ɗin ƙasar Habashan ya jiyo wata majiyar sojin ƙasar Habashan tana cewa sojojin gwamnatin sun kashe ‘yan tawayen jam'iyyar TPLF ɗin guda 15 da kuma kama wasu guda 8 ciki kuwa har da tsohon shugaban yankin Abay Weldu da kuma wani tsohon shugaban jam’iyyar ta TPLF.

Wasu majiyoyin kuma sun ce daga cikin waɗanda aka kashe ɗin har da tsohon mataimakin kwamishinan ‘yan sandan yankin wanda ake nema ruwa a jallo.

A ƙarshen watan Nuwamban shekarar bara ta 2020 ne dai gwamnatin Habashan ta sanar da samun cikakkiyar nasara kan jam’iyyar Tigray People’s Liberation Front (TPLF), da ke riƙe da yankin Tigray bayan yaƙin da ya ɓarke tsakanin dakarun gwamnati da na ‘yan tawayen.

Wannan Sanarwa ta baya-bayan nan ɗin dai da sojojin suka yi ta zo bayan da a ranar Juma’ar da ta gabata sojojin suka sanar da kame ɗaya daga cikin manyan ƙusoshin jam’iyyar ta TPLF kuma daga cikin waɗanda suka ƙirƙiro ta wato Sebhat Nega, kamar yadda kuma gidan talabijin ɗin ya ce an kama tsohon mataimakin shugaban ƙasar ma Abraham Tekeste. Sai dai har ya zuwa yanzu ba a tantance inda shugaban jam’iyyar, Debretsion Gebremichael da sauran manyan ƙusoshinta da kwamandojin sojojin yankin suke ba tun bayan da suka ɓuya bayan da gwamnatin Habasha ta sanar da cewa tana neman su ruwa a jallo bayan dakarun gwamnatin sun kame babban birnin yankin

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!