Messi Ya Zama Dan Wasan Da Ya Fi Cin Kwallaye A Gasar La Liga Ta Kasar Spain

2021-01-11 14:09:00
Messi Ya Zama Dan Wasan Da Ya Fi Cin Kwallaye A Gasar La Liga Ta Kasar Spain

Kyaftin ɗin ƙungiyar kwallon ƙafa ta Barcelona, Lionel Messi, ya ɗare mataki na ɗaya a cin kwallaye a gasar La Liga ta ƙasar Spain bayan kwallaye biyu da ya zura a wasan da ƙungiyar Barcelona ta buga na ƙarshe da ƙungiyar kwallon ƙafa ta Granada.

A yayin wannan wasan dai Barcelona ta yi nasara a kan Granada da ci 4-0 inda Messi ya zuwa kwallaye biyu a wasan, wanda hakan ya sanya shi a mataki na farko na ‘yan wasan da suka fi cin kwallayen da kwallaye 11.

Dan wasan kwallon kafa na Villareal, Gerard Mreno shi ne ke biye masa da ƙwallaye 10 sai kuma ‘yan wasan nan Luis Suarez da Lago Alpas da suke da kwallaye tara-tara sai kuma dan wasan kungiyar kwallon ƙafan nan ta Real Madrid Karim Benzema da ked a kwallaye takwas.

A halin yanzu dai ƙungiyar kwallon ƙafa ta Atletico Madrid ita ce a kan gaba a teburin gasar na La Liga da maki 38 sai kuma Real Madrid ta biyu da maki 37 sai kuma Barcelonan mai maki 34.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!