Iraki:Shugaban Kasa Ya Gana Da Shugaban Hashdushaabi Falih Al-Fayyad

2021-01-11 10:00:03
Iraki:Shugaban Kasa Ya Gana Da Shugaban Hashdushaabi Falih Al-Fayyad

Shugaban kasar Iraki Barham Saleh ya gana da shugaban rundunar Hashduahaabi na kasar bayan da gwamnatin kasar Amurka ta sanya masa takunkumin tattalin arziki. Kamfanin dillancin labaran Fars na kasar Iran ya nakalto shugaban kasar yana cewa gwamnatin kasar Iraki ba zata taba amincewa da shishigi cikin al-amuran cikin gida na kasar ba.

Kafin ganawar jami’an gwamnatin guda biyu a jiya Lahadi dai, a ranar jumma’ar da ta gabata ce ma’aikatar kudin Amurka ta sanya sunan Falih Al-Fayyad cikin jirin mutanen wadanda ta sanyawa takunkuman tattalin arziki, saboda a binda ta kira wai take hakkin bil’adama.

A shekarara da ta gabata ce gwamnatin kasar Amurkan ta kashe mataimakin Falih Fayyad, wato Abu Mahdi Al-Muhandis tare da bakon gwamnatin kasar Iraki Shaheed Qasim Sulaimani a tashar sauka da tashin jiragen sama na Bagdaza.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!