Najeriya: Buhari Ya Bukaci Manya-Manyan Jami’an Wasanni, Limamai Da Pasto-Pasto Su Yi Alluran Riga Kafin Korona

2021-01-11 08:59:07
Najeriya: Buhari Ya Bukaci Manya-Manyan Jami’an Wasanni, Limamai Da Pasto-Pasto Su Yi Alluran Riga Kafin Korona

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci jami’an wasannin motsa jiki na kasa da limamai da kuma Pasto-Pasto su yi alluran riga kafin cutar korona a gaban jama’a a gidajen talabijin na kasa, don kwadaitar da mabiyansu yin hakan.

Gwamnan jihar Ikiti Kayode Fayemi ne ya bayyana haka a bayan ganawarsa da shugaban kasar a fadarsa a jiya Lahadi.

Kafin haka dai an bada sanarwan cewa, shugaban kasa da mataimakinsa da kuma sakatarin gwamnatin tarayyar da sauran manya-manya jami’an gwamnati zasu yi allurer riga kafin a tashar talabijin ta kasa wato NTA saboda kwadaitar da sauran mutanen kasar yin alluran .

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!