Yemen: Amurka Zata Sanya Ansarullah Ta Kasar Cikin Jerin Kungiyoyin ‘Yan Ta’adda A Wajenta

2021-01-11 08:49:49
Yemen: Amurka Zata Sanya Ansarullah Ta Kasar Cikin Jerin Kungiyoyin ‘Yan Ta’adda A Wajenta

Majiyoyin labarai daga kasar Amurka suna cewa gwamnatin kasar zata sanya kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen a cikin jerin kungiyoyin yan ta’adda a wajenta.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyoyi biyu, wadanda aka amince da labaransu suna cewa, mai yuwa a yau litinin ne gwamnatin shugaban Donal Trump zata sanya kungiyar ta Ansarallah cikin jerin kungiyoyi masu tallafawa ayyukan ta’addanci a wajenta.

Jami’an diblomasiyya da kuma kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa sun nuna damuwarsu dangane da daukar wannan matakin, saboda yana iya shafar tattaunawar sulhu wanda MDD take jagoranta tsakanin Yemen da kuma Saudiya sannan mai yuwa hakan ya shafi ayyukan bada agaji wadanda kungiyoyin kasa da kasa suka gudanarwa a kasar ta Yemen.

Tun shekara ta 2015 ne gwamnatin kasar Saudia take kokarin kifar da gwamnatin kasar Yemen da nufin maida tsaohon shugaban kasar kan kujerar shugabancin kasar, amma ta kasa yin hakan saboda turjiyarda Ansarullah da kawayenta suke nunawa.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!