Iran : Majalisar Dokoki Ta Haramta Shigo Da Rigakafin Covid-19 Na Amurka Da Biritaniya

2021-01-10 21:13:18
Iran : Majalisar Dokoki Ta Haramta Shigo Da Rigakafin Covid-19 Na Amurka Da Biritaniya

‘Yan majalisar dokokin Iran, sun goyi bayan matakin da jagoran juyin juya halin musulinci na kasar ya dauka na haramta shigo da riga kafin cutar korona daga kasashen Amurka da Biritaniya.

A wata sanarwa da majalisar ta fitar yau Lahadi, ta ce kokarin da kwararun ‘yan kasar ke yi wajen samar da riga kafin korona abun yabo ne kuma tamakar martabar kasar ne.

‘Yan majalisar sun ce a lokacin da Iran ke cikin matsin lamba na takunkumi, sannan kuma kasashen turai suka ki amince mata shigo da kayan asibiti hatta wannan takunkumin na rufe fuska, wannan matakin da jagora ya dauka na haramta shigo da maganin Amurka da Biritaniya ya yi daidai.

Tun dai lokacin da korona ta bulla a kasar ne, Iran ta shiga aiki tukuri wajen kera kayayakin da take bukata wajen yaki da annobar.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!